Kifi halitta ce daga cikin halittun da ake samu a ruwa, yana daya daga cikin sanannun halittun ruwa, kifi yana da jinsi iri-iri fiye da nau'uka 71 a duniya musamman kifayen dake kwance a teku musamman irinsu tekun atlantika da bahar maliya, lallai akwai nau'ukan kifaye wadanda har yanzu dan adam bai gama gano su ba.